Fagen zamantakewa

Fagen zamantakewa

9 darussa

Wannan fage ne dake bada kulawa wajen samar da alaqar zamantakewa dedetatta tsakanin musulmai, sannan tsakanin musulmi da wanda ba su ba na sauran ma’abuta adddinai, ta hanyar samar da alu’ma mai tafiya kan tsarin musulunci,ta yadda ko wane mutum zai san menene ke gare shi kuma menene a kanshi na wajibbai. Hakan sai ya samar da alu’ma ta musulunci mai alaqa gwaggwa’ba da juna .

Nasiha da amana

Nasiha itace kashin-bayan addini, domin addinin gaba dayan shi nasiha ne, kuma nasiha tana kasancewa ne ga Allah, da manzonsa, da shuwagabannin musulmi, da gama-garinsu. Dukkan sanda mutum yayi nasiha game da wadannan abubuwa, ta addini ya cika, kuma duk wanda yayi sakaci wajen nasiha ga wani cikin wadannan abubuwa, to hakika addininsa ya samu tawaya gwargwadon sakacinsa. Don haka wajibi ne musulmi ya lura da amana wajen nasihar da ze gabatar, da bayanin gaskiya ba tare da yin kara ba ga kowaye, domin shi yana cikin kariyar Allah.

0
Haqqin musulmi akan musumi dan-uwansa

yan'uwantaka don Allah niima ce babba daga Allah, kuma wata irin falala ce da Allah ke kwararota da kyautarta ga bayinsa muminai masu gaskiya. Yanuwantaka abin sha ne me tsarki da Allah ke shayar dashi ga muminai tsarkaka. Hakika musulunci ya zaku wajen karfafa dankon zumunci tsakanin musulmi da dau-uwansa, don haka ne ma ya sharanta wasu alamura da zasu karfafa wannan alaka, kamar yada sallama, da gaida marasa lafiya, da dai sauran hakkokin musulmi akan musulmi dan uwansa.

0
Bin iyaye da barin saba masu

Hakkin hakkin iyaye yana nan daram, kuma zamantakewa tagari dasu wajibi ne, koda kuwa sun kasance kafirai, hakanan musulunci ya tsawatar daga saba masu matukar tsawatarwa, don haka ya sanya saba masu daga cikin mafi girman lefuka bayan shirka da Allah madaukakin sarki, kai har ma musulunci ya fifita hadimar iyaye akan jihadi wajen daukaka Kalmar Allah, wanda shine kololuwar musulunci.

0
Zakka da gudumawar da take bayarwa wajen taimakon alumma

waye a cikinmu baya son a kara masa arzikinsa, dukiyarsa ta karu? Allah ya tsarkake masa ita, ya yi masa albarka a cikinta? To ku taho zuwa ga abin yake sanya haka, wannan abu ba komai ba ne face bayar da zakka.

0
Abota Ta Kwarai Da Tasirinta Ga Mutum

Bayan haka: Ya bayin Allah! Hakika musulunci addni ne da yake da nagartattun 'dabi’u, don haka ya dace da 'dabi’un da ba a gur'bata su ba. Ya kuma dace da 'dabi’un da suke masu kyawu. Musulunci shi ne maganin gur'batattun 'dabi’u

0