Fagen munasabobi

Fagen munasabobi

5 darussa

Wannan fage ne dake bada kulawa wajen bayanin hukunce-hukuncen musulunci game da munasabobin shekara, kamar idin karamar sallah da sallar layya, da kisfewar rana ko wata, da sauran su. hakanan zamu yi bayanin sabawa sharia da wasu cikin musulmi kan aukawa lokacin wadannan munasabobi.

Bikin idin karamar sallah

idi a musulunci yana da manufa mai girma, da karamci da cikakken amfani, da maslaha ta duniya da lahira. Musulunci yana da idi guda biyu. Idin karamar sallah da idin babbar sallah. Kuma dukkansu suna zuwa ne bayan wata ibada mai girma, kuma a bayan wani rukuni daga cikin rukunan musulunci, kuma akan yi shi a mafificin lokaci.

0
bikin (idin) babbar salla

Hakika idin babbar sallah idi ne na layya, kuma idi ne na karamci da tausayawa ga mabukata, wani irin idi ne wanda miliyoyin musulmi suke haduwa domin aiwatar da mafi girman shaira (alama cikin alamomin addini) wato hajji. Haka nan a idin layya ne karamcin masu karamci ke bayyana wajen layya da yanka, domin neman kusanci zuwa ga Allah, da kuma rabawa matalauta da mabukata.

0
Sallar rokon ruwa

Fari alama ce ta nisan mutane da biyayya ga Allah, kuma alama ce a fili ta keta dokokin Allah madaukakin sarki. Don sabawa Allah na janyo sharri da hallaka albarkatu. Yana daga cikin rahamar Allah ga bayin sa yanda ya sharanta musu sallar rokon ruwa, domin su dawowa ubangijin su, kuma su fake da shi domin ya yaye musu abinda ya same su, sai kaga ruwa na sauka saboda rahamar Allah da bayin sa.

0
Kisfewar rana da wata

lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, wadanda suke nuni ga cikar kudurarsa, da cikar kamalarsa da hikimarsa da rahamarsa. Idan ka yi dubi girmansu, da tsarin tafiyarsu, za ka gane girman kudurar Allah. Kuma idan ka yi dubi maslaha da amfanin da ke cikin sabawa a cikin tafiyarsu, za ka tarar cewa a cikin wannan akwai cikar kamala da rahamar Allah. Ku saurara! Yana daga cikin hikimar Allah a wajen tafiyarsu abin da yake faruwa na kusufi, wanda shi ne gushewar haskensu gaba daya, ko wani sashensa. Lallai hakan yana faruwa ne da umarnin Ubangiji. Allah yana tsoratar da bayinsa da shi, domin su tuba zuwa gare shi su nemi gafararsa, su bauta masa, su girmama shi.

0
Hudubar sabuwar shekara

Ya kai masoyi, ka yi duba zuwa ga shafukan rayuwarka da ta shude, mai ka aje a cikinsu domin lahirarka? Ka yi tunani a ranka,:me wannan harshe naka ya fada? Me kuma idanunka suka kalla? Kunnen nan naka me ya ji? Kuma wadannan kafafuwan naka ina suka je? Ya hannu! Me kika taba? Abin da ake bukata a gurinka shi ne ka rike linzamin rayuwarka da kanka. Ka yi wa kanka hisabi.

0