Fagen kira zuwa ga Allah

Fagen kira zuwa ga Allah

5 darussa

Wannan fage ne dake bada kulawa wajen yada musulunci a dukkan duniya, ta hanyar kafafen yada labarai daban-daban. hakan kuwa ta hanyar bayanin muhimmancin kira zuwa ga Allah, da hanyoyin kiran ingantattu, da darajojin umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, tare da bijiro da manhajar manzanni wajen kira zuwa ga Allah, manhajar da take tsaka-tsaki kuma daidaitacciya.

Kwadaitarwa wajen neman ilimi da aiki da shi

Ilimi haske ne da shiriya, kamar yadda jahilci duhu ne da bata. Ilimi idan ya hadu da imani, daukaka ne duniya da lahira, kuma aiki shine ribar ilimi, kuma shine asasin ilima da gayar sa, don haka ya wajaba ga daliban ilimi yin aiki da iliminsu, in ba haka ba kuwa, sai ilimin ya zama hasara gare su kuma mara amfani,domin malamin da baya aiki da ilimin shi, kamar fitila ce haska wani kona kanki.

0
Tafarkin kira zuwa ga Allah

Yana daga cikin fitattun bangarori a cikin rayuwar annabawa, bangaren kira zuwa ga Allah madaukakin sarki, kuma wannan kira yana da tafarkinsa wanda yake bayyananne da babu rudani a ciki. Daga ciki akwai: ilimin abinda mutum ke kira zuwa gare shi, da aiki da abinda yake kira zuwa gare shi, da kaddamar da abu mafi muhimmanci sannan me bi masa, da siffatuwa da dabiu kyawawa, hade da sanya hikima yayin kira zuwa ga Allah.

0
Kafafen yada labarai da tasirinsu a cikin rayuwar mutane

Kafafen yada labarai da nauoinsu daban-daban suna da matukar tasiri wajen tsara tinanin yara masu tasowa da iyalai da aluma gaba dayanta. Hakuwa na faruwa ne saboda abinda suke yadawa mai cike da hanyoyin tasiri da daukan hankali sosai, don haka ya zama wajibi a ribace su ribatar da ta dace, da rikarsu a matsayin wani minbari yada daawa, da yada dabiu ingantattu na musulunci

0
Muhimmancin umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummuna

Umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna aiki ne babba, da yawan muttane sun gafala daga barin shi. Lallai ba karamar annoba bace wadda karshenta ba zaiyi kyau ba ga daidaikun mutane da aluma gaba-daya, yayin da daliban ilimi da shiryayyun matasa zasuyi ko-in-kula da kutsawa cikin fagagen gyara na rayuwar yau da gobe, don umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna.

0
Hanyoyin Mallake zukatan masu saurare

Muamala da zukata domin mallakewa da kame su, wata mahara ce da ke bukatar mutum ya kware ta bangaren,kuma mutumin dake so ya kai ga gaci da samun nasara wajen muamala da zukatan mutane, dole ne ya san yare da mabudin zukata, domin kowacce zuciya nada mabudinta, wanda in ba dashi ba, to ba yadda za ai a shiga cikin ta. Daga ciki akwai murmushi, da tarba da sallama, da kyauta, da sauransu.

0