Kisfewar rana da wata

Kisfewar rana da wata

lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, wadanda suke nuni ga cikar kudurarsa, da cikar kamalarsa da hikimarsa da rahamarsa. Idan ka yi dubi girmansu, da tsarin tafiyarsu, za ka gane girman kudurar Allah. Kuma idan ka yi dubi maslaha da amfanin da ke cikin sabawa a cikin tafiyarsu, za ka tarar cewa a cikin wannan akwai cikar kamala da rahamar Allah. Ku saurara! Yana daga cikin hikimar Allah a wajen tafiyarsu abin da yake faruwa na kusufi, wanda shi ne gushewar haskensu gaba daya, ko wani sashensa. Lallai hakan yana faruwa ne da umarnin Ubangiji. Allah yana tsoratar da bayinsa da shi, domin su tuba zuwa gare shi su nemi gafararsa, su bauta masa, su girmama shi.